Najeriya: Fashe-fashen rumbunan ajiyar kayan abinci
October 26, 2020Kama daga yankin arewacin Najeriya ya zuwa yankin kudu ake ci gaba da farfasa rumbunan ajiya na gwamnatoci na jihohi dama na masu kasuwa da sunan wasoson kayan masarufi a jihohi dabam-dabam. A Abuja dai wasoson ya ci gaba har ya zuwa wannan Litinin a garin Gwagwalada inda wasu matasa suka farma rumbunan ajiyar kayayyakin suka wawashe kayan amfanin gona.
Duk da cewar dai sannu a hankali al'adar wasoson na dada bazuwa ya zuwa jihohin arewacin kasar, daga dukkan alamu abun da ke faruwar ba shi ruwa da tsaki da batun yunwar da ake ta'allakawa da karuwar tashi na hankalin. Can a jihar Yobe da ke zama daya a cikin jihohin da ko bayan Covid-19, suke kuma fuskantar tashin hankali na ta'addanci.
An dai share wunin wannan rana ana wani taron gaggawa na majalisar tattalin arziki ta gwamnoni na kasar, bayan zargin boye kayan na tallafi a bangare na gwamnonin kasar da ke da mallaki na rumbunan ajiyar. Amma a cewar Abdurazak Bello Barkindo da ke zaman kakaki na kungiyar gwamnoni ta kasar, akwai rashin na fahimta ga masu zargin gwamnonin da boye kaya a cikin tsakiyar hali na bukata.
To sai dai kuma akwai fargabar yiwuwa a ci guba a tsakani na dubbai na matasan da suka wasashe abubuwa dabam-dabam, kama daga shi kansa abincin ya zuwa ga irin shuka, dama sinadarai da sunan korar yunwar.Tarrayar Najeriyar dai na a tsakanin dadadawa matasan da ke ci gaba a cikin karatun rikici da kuma fuskantar makoma mara tabbas sakamakon rikidewar bukatun ya zuwa wasoso na dukiyar al'umma.