1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Tiani ta bankado 'yan fanshon boge 3000

Salissou Boukari MAB
November 18, 2024

Bincike da aka gudanar kan ‘yan fansho ya bankado yawan mutanen da ake biya ta barauniyar hanya, inda aka gano wasu sun jima da rasuwa, wasu kuma an rubunya sunayensu. Lamarin da ya janyo wa gwamanti asarar kudi.

https://p.dw.com/p/4n7KM
Janar Abdourahamane Tiani na Jamhuriyar NIjar
Janar Abdourahamane Tiani na Jamhuriyar NIjarHoto: ORTN/Télé Sahel/AFP/Getty Images

Umarnin da shugaban kasa da firaminista wanda kuma shi ne mninistan kudi naNijar  suka bayar ne, ya ba da damar tantance adadin ma’aikatan da suka yi ritaya a zahiri, da kuma adadin kudaden da ya kamata a biya su cikin ka’ida, ba tare da bata wani lokaci ba, Sai dai shugabar baitil'malin Nijar Madame Seidou Zeinabou Douka ta ce sun saka kwararru da suka yi binciken ma’aikatan da suka yi ritaya ta hanyar takardunsu da kuma ganin su a zahiri, inda daga bisani aka gano tarin kura-kurai cikin lamarin da ke haddasa asarar kudi sama da CFA miliyan 500 a wata ga gwamnati.

Yawan 'yan fansho na boge da aka gano a Nijar

Zeinabou Douka ta ce: " A jimlance, mutane dubu 3113 ne aka gano suna karbar kudin fansho ba bisa ka’ida ba, daga cikin ma’aikatan da suka yi ritaya da ake biyan kudi miliyan 540 a kowane wata. Don haka a karshen wannan bincike da wadannan kwararru da kuke gani a gabanku suka yi, ya ba mu damar  tsaftace jerin sunayan 'yan fansho na kasa. Sannan a daya hannun, zai ba mu damar soke wadannan mutane sama da dubu uku da ake biya ba bisa ka’ida ba."

Karin bayani:  Sabuwar dokar fansho a Najeriya

Firaminista Ali Mahaman Lamine Zeine ne ya ce a gudanar da bincike kan 'yan fansho
Firaminista Ali Mahaman Lamine Zeine ne ya ce a gudanar da bincike kan 'yan fanshoHoto: DW

Ra‘ayoyin 'yan Nijar sun bambanta dangane da wannan aiki na binciken 'yan fansho, inda wasu daga cikin masanna tattalin arziki da  suka yi ritaya irin su Issoufou Boubakar kado Magaji, ke ganin cewa,  sakamakon wannan bincike ya nunar a fili cewa da sauran rina a kaba wajen samun gaskiyar yawan 'yan fansho na boge. Sai dai 'yan kungiyoyin farar hula da ke fafutukar ganin gwamnati ta tsaftace duk ma’aikatu domin kasa ta ci-gaba, irin su Bana ibrahim na ganin cewar ya kyautu gwamnati ta fadada wannan bincike ga sauran ma’aikata ba wai 'yan ritaya kadai ba.

Me makomar masu hannu a ta'asar 'yan fansho?

Ba a san matakin da gwamnatin mulkin sojhan Nijar za ta dauka a kan wadanda ke da ruwa da tsaki wajen tafka wannan ta’asar kudin 'yan fansho ba. Amma akasarin 'yan kasar na ganin cewa, karancin hukunta masu laifi ne ke bai wa sauran ma’aikata damar ci gaba da miyagun ayyukan da suke yi a cikin ma’aikatu na gwamnati.