1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Sudan ta bijire wa taron sulhu

July 10, 2023

Sojojin gwamnatin rikon kwaryar Sudan sun ki karbar goron gayyata i zuwa zaman tattaunawa a kan rikicin kasar wanda aka kammala a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

https://p.dw.com/p/4ThEH
Taron kasashen IGAD a Habasha
Taron kasashen IGAD a kasarHabashaHoto: Office of the PM Ethiopia

Kungiyar kasashen gabashin Afirka IGAD mai kasashe mambobi hudu da suka hadar da Kenya da Jibuti da Habasha da kuma Sudan ta Kudu ce ta shirya taron na yini guda wanda ya samu halartar wanda ya samu halartar bangaren dakarun RSF masu biyayya ga tsohon mataimakin shugaban Sudan din Janar Mohamed Hamdane Daglo.

A sanarwar da ta fidda bayan kammala zaman, kungiyar ta nuna rashin jin dadinta kan rashin halartar bangaren janar Abdel Fattah al-Burhane wanda tun da farko ya nuna amincewa da karbar goron gayyatar.  Kungiyar ta kuma yi kiran da a sake rattaba hannu kan yerjejeniyar tsagaita bude wuta don kawo karshen asarar rayuka da fadan ke ci gaba da haddasawa.

Daga karshe kungiyar ta IGAD ta bukaci reshenta na EASF mai kula da bangaren tsaro da ya zauna nan gaba don duba yiwuwar aika runduna ta musanman i zuwa Sudan din domin bayar da kariya ga fararen hula da kuma damar kai kayan agaji.