Najeriya: Takaddama kan dauke wuta yayin yajin aiki
June 7, 2024A yayin da ake saran komawa bisa teburin tattaunawa a tsakanin gwamnatin Najeriya da masu kwadagon kasar, tuni aka fara nunin yatsa a tsakanin gwamnatin da ke zargin su da zagon kasa ga kasar, da kuma masu kodagon da ke fadin ba dai dai.
Kuma a cikin tsakiyar rikicin dai na zaman matakin masu kwadagon na dauke wutar lantarki a lokaci na yajin aikin. Masu kwadagon dai sun tilasta wa ma'aikata na kamfanin rabon wutar kasar TCN tsaida aiyuka tare da kulle cibiyoyi na wutar a daukacin kasar a lokacin yajin aiki.
Abun kuma da ya bata ran 'yan mulkin dake fadin masu kodagon sun wuce gona cikin iri cikin batun wutar dake zman ruhi na tattali na arziki d akila ma tsaron kasar. Abdullahi Tanko dai na bai wa shugaban kasar shawara cikin lamura na kasar.
"In ka kashe wutar nan, kafin ta dawo ta yi dai dai, sai an yi kwana da kwanaki. In baka manta ba lokacin Janar Ibrahim Babangida 'yan kwadago sun taba wannan, sai da aka daure su. Ba a hana yajin aiki ba, amma ta kai har ga kashe wutar kasa ha'inci ne".
Neman hanyar daure masu kwdago, ko kuma kokari na murde wuya, ana dai kallon zargin da idanu na kokari na murde wuya ta masu kwadagon da ke dada nuna alamun tsaiwa irin ta gwamen jaki cikin batun tattaunawar.
Dr Muttaka Yusha'u dai na zaman shugaba na gangami a kungiyar ta kwadagon kasar wato NLC. Kuma ya ce yajin aikin ba shi da banbanci walau a bangaren wutar lantarkin dama ragowar ma'aikatan kasar.
"Wannan magana ta zo mana da mamaki, ma'aikata ne kawai suka janye aikinsu, kuma ba na wutar lantarki ba, kowa ya shiga, ba kuma abu ne sabo ba, ma'aikata su janye aikinsu. Amma ba mamaki saboda wannan hanyoyi ne da gwamnati ta bullo da su domin hada 'yan kasa da masu kwadago".
Koma wane tasiri dauke wutar ta kai ga yi cikin tarayyar Najeriyar dai, tuni dai da ma wutar kasar ta kai ga rushewa, tun ma kafin tsundumar ma'aikatan cikin yajin aikin a fadar Comrade Sikamta Ali da ke zaman mataimakin sakatare na kungiyar ma'aikatan wutar kasar.
"Da ma mutum ne ke zama yana lura da wuta, kuma shi ma ya janye aikinsa bisa umarni da biyayya da yake yi. Ko da basu janye ba wuta da kanta zata tafi. Saboda babu mai kula da ita. Kuma ma'aikatan nan basu fara yajin aiki ba sai kusan karfe 6-7 na safiyar Litinin, kuma wutar ta tafi tun karfe 2:19 na dare, ta yaya za'a ce ma'aikata ne suka dauke ta da gangan".
A karkashin dokar Najeriya dai batun na zagon kasa ga kasa dai na iya kaiwa ga hukuncin dauri har karshen rai. Barista Badamasi Sulaiman Gandu dai na zaman wani lauyan da ke zaman kansa a tarayyar Najeriyar.
"Dauke wutar lantarki gaba dayanta lokaci guda ba karamin laifi ba ne, saboda ya shafi bangarori guda uku na farko ya shafi batun tsaro, da lafiya da tattali na arziki. Shi yasa ni ma ina tare da gwamnatin tarayya a kan cewar abun da 'yan kwadagon suka yi sun wuce gona da iri".
'Yan awoyin da ke tafe dai na da tasirin gaske cikin takaddamar ga masu kwadagon da wa‘adin yajin aikinsu ke zaman karshen wannan mako.