1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin hadaka tsakanin CDU da SPD

October 20, 2013

Kwanaki biyu kafin wa'adin gwamnatin Jamus ya cika, an gaza cimma wata kwakkwarar matsaya a gwamnatin hadaka da ake kokarin kafawa tsakanin CDU da SPD.

https://p.dw.com/p/1A2mC
Hoto: picture-alliance/dpa

Bukatar kafa gwamnatin hadaka ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da jam'iyyar adawa ta SPD na fuskantar gagarumin kalubale, biyo bayan babban taro da jam'iyyar SPD din ke gudanarwa wanda a shine za ta kada kuri'ar amincewa da shiga gwamnatin hadakar da jam'iyyar CDU ta Angela Merkel ko kuma akasin hakan.

Duk da cewa jam'iyar adawar ta SPD bata da wani kwarin gwiwa da karsashin kafa gwamnatin hadaka da CDU, sai dai shugabannin jam'iyyar na da tabbacin cewa wakilan jam'Iyyar sama da 200 da ke halartar taron za su kada kuri'ar amincewa da bukatar.

Jam'iyyar ta SPD dai na bukatar a bunkasa samar da aiyukan yi da Ilimi da kudaden sallama daga aiki a bangarori da dama da kuma yin gyara gwamnatocin gundumomi. Sai dai a kwai yiwuwar su ajiye sharadin karawa masu hannu da shuni yawan kudaden harajin da suke biya, bisa yarjejeniyar amincewa da mafi karancin albashi na Euro 850 duk awa guda.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Zainab Mohammed Abubakar