1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Haramta aikin hakar ma'adanai a Zamfara

April 8, 2019

Hukumomin a Najeriya sun bayyana daukar matakai na hana hakar ma'adanai saboda tabarbarewar tsaro da kashe-kashen al'umma a Jihar Zamfara.

https://p.dw.com/p/3GTJ4
Gold waschen in Bagega Zamfara Nigeria
Hoto: Aminu Abdullahi Abubakar

Gwamnatin Najeriya ta dakatar da hakar ma'adanan karkashin kasa a Jihar Zamfara tare da korar 'yan kasashen waje masu aikin hakar ma'adanan sakamakon matsalolin tsaro da kashe-kashen al'umma da ake fama da su a Zamfara.

Hukumomin jihar na zargin cewa ana fakewa da hakar ma'adanan ne don yi wa 'yan bindigar safarar makamai, idan aka yi la'akari da kin bayar da hadin kai da masu hakar ma'adanan ke yi domin gano masu kai hare-haren a dazukan da suke aiki. Sannan kuma hukumomin na cewar duk hare-haren da ake kai wa Al'umma ba'a taba kai masu ba.

Sau tari dai al'ummar Jihar Zamfara na kokawa da rashin cin moriyar arzikin ma'adanai da Allah ya albarkanci yankin da shi tare da cewar ba sa samun riba ko daya, ko da yake ana samun ra'ayoyi masu cin karo da juna kan matakin korar masu hakar ma'adanan. Gwamantin Najeriya ta dade tana daukar matakai dabam-dabam masu nasaba da tsaro a Jihar Zamfara.