1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gurɓataccen ɗanyen mai na cigaba da malala a tekun Mexico

April 29, 2010

Malalar ɗanyen mai a tekun Mexico na cigaba da haifar da damuwa.

https://p.dw.com/p/N9SZ
Ma'aikatan agaji na cigaba da ƙoƙarin kwashe ɗanyen man da ya malala a tekun Mexico.Hoto: AP

Mako guda bayan haɗarin fashewar bututun mai a mashigin tekun Mexico na ƙasar Amirka wanda ya yi sanadiyar malalar dubban lita na danyen mai a cikin tekun, har yanzu maáikatan agaji waɗanda su ka yi amfani da naura mai sarrafa kanta domin kaiwa ga bututun sun kasa toshe wurin da ya huje.

A yanzu dai maaikatan agajin sun fara gina wata katafariyar rumfa a ƙarkashin tekun domin rufe sunduƙin haƙar man da ya nutse a ƙarƙashin tekun. Shi kansa wannan aikin gina rumfar ana sa ran zai ɗauki tsawon makonni huɗu a cewar jami'an kula da tsaron gaɓar ruwan na Amirka.

Ko da ta sama ta hangi tekun za ka ga zirin baƙin layi akan ruwan ya miƙe iya ganinka. Faɗin da'irar da man ya malala a cewar wasu masana ya fi faɗin jihar Rhode Iceland ta ƙasar Amirka wanda hakan ya sa ya zama aiki gagarumi kuma mawuyayi wajen shawo kansa, bugu da ƙari jirgin saman Jami'an tsaron gaɓar ruwan Amirka ƙirar C130 zai iya yin feshin magani ne kawai ta sama a inda man ya malala akan teku domin tattara man wuri ɗaya yadda za'a iya kwashewa cikin sauƙi amma ba zai iya yin feshe a ƙarƙashin ruwa inda man ya malale tsakanin Louisiana da Florida ba a cewar shugaban hukumar kula da mashigin kogin Doug Helton " Za mu dakatar da a aikin hasashe a kwanaki uku masu zuwa yayin da za mu cigaba da gudanar da wasu ayyuka a kogin".

Sai dai a yayin da muhimman wurare na gaɓar kogin dake zama muhalli ga tsuntsaye da tsirai da sauran hallitu a yankin ke fuskantar barazanar mawuyacin yanayi, hatta su kan su masana sun baiyana cewa babu wata hanyar da za'a kare illar da kwararar ɗanyen man zai iya yi ga muhallin tsiran a ƙarƙashin teku yayin da dubban gallon na gurɓataccen man ke cigaba da malala a mashingin kogin na Mexico. Shi ma wani mai sharhi kan harkokin mai a mujallar Wall Street Guy Chazan yayi bayani da cewa" Baá taɓa yin aiki mai zurfi irin wannan ba.

A yanzu haka dai Jami'an kula da tsaro a gaɓar kogin na amfani da naurori masu sarrafa kansu har guda takwas domin toshe inda man ke tsiyaya don kare cigaba da yaɗuwarsa. Babbar jami'ar dakarun tsaron gaɓar tekun Real Admiral Mary Landry wace ke shugabatar gagarumin aikin tsabtace kogin ta ce idan aka kyale al'amarin zai zama ɗaya daga cikin kwararar mai mafi muni da aka taɓa samu a tsawon tarihi a ƙasar Amirka.

Mawallafa :  Ralph Sina / Abdullahi Tanko Bala

 Edita       : Yahouza Sadissou Madobi