Uwargidan Laurent Gbagbo za ta gurfana a gaban kuliya
March 18, 2016Talla
Simone Laurent Gbagbo da ake mata lakabi da Iron Lady mai shekaru 66, tuni aka yanke mata hukuncin zaman gidan yari a shekarar da ta gabata kan irin rawar da ta taka a dangane da rikicin bayan zaben kasar da ita da mai gidanta a shekara ta 2010. Kotun Kasa da Kasa da ke Hukunta masu Aikata Manyan Laifuka wato ICC da ke da zama a birnin The Haque na kasar Neatherlands ma dai ta bada sammacin kamo Simon Gbagbo, koda yake kawo yanzu gwamnatin ba ta mika ta ba. Duk dai da matsin lambar da kotun ta ICC ta yi na a mika ta, shugaban kasar ta Cote d'ivoire Alassane Ouattara ya yi kememe a inda ya ce bangaren shari'ar kasar ma zai iya yanke mata hukunci cikin adalci.