1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari'ar masu zanga-zanga na shan suka a Najeriya

Uwais Abubakar Idris MAB
September 2, 2024

Kungiyar Amnesty International ta yi Allah wadai da fara shari’ar matasa da suka gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa. Fiye da matasa 1000 da aka kama ne ke fuskantar zarge-zargen tayar da tarzoma da cin amanar kasa.

https://p.dw.com/p/4kBKs
Dubban matasa ne suka gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa a biranen Najeriya
Dubban matasa ne suka gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa a biranen NajeriyaHoto: Sunday Alamba/AP/picture alliance

Matasan da aka kama a lokacin zanga –zangar tsadar rayuwa ta tsawon kwanaki goma ne ke fuskantar  shari'a a kan zargin aikata laifuffuka iri-iri a kotunan Najeriyar da ke biranen Abuja, Kano, Kaduna da Maiduguri. Dagewa a kan wannan tuhuma da ake yi masu, duk da turjiya daga kungiyoyin kare hakkin jama'a da ma lauyoyi da ke fafutukar kwatar ‘yanci irin su Femi Falana ya sanya lamarin daukar hankali sosai.

Karin bayani:  Najeriya: Zanga-zanga na daukar sabon salo

Kungiyar Amnesty International da ke Najeriya ta yi Allah wadai da wannan shari'a, inda daraktan kungiyar a Najeriya Isa Sanusi ya ce: " Mun hango cewar ana so a mayar da mutane su zama kamar ba su da 'yanci a kasar nan. Idan ka yi zanga-zanga, hukuma za ta fito ta ci ma mutunci, a yi ma duka, wasu a kashe su. Sannan wadanda aka kama, a je a yi musu shari'a kuma a daure su."

Jami'an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zanga
Jami'an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangaHoto: Kola Sulaimon/AFP

Gwamnatin Najeriya na tuhumar matasan da aka kama da aikata laifuffuka guda goma, ciki har da cin amanar kasa da yunkurin kifar da gwamnati da tunzura jama;a ga yin bore. Wadannan laifuffuka ne da za su iya sa su fuskanci hukuncin da aka tanada a sassa  96 da 97 na dokar Penal Code ta Najeriya.

 "Idan zanga-zanga laifi ne... dimukuradiyya ma laifi ne"

Wasu daga cikin matasan da suka gudanar da zanga-zangar sun bayyana rashin jin dadinsu game da halin da 'yan uwansu suka shiga. Comrade Yahya Abdullahi da ke cikin wadanda suka jagoranci zanga-zangar, ya ce: "An gurfanar da wasu abokanmu da 'yanci da dokar kasa suka ba su damar fita kan titi domin gudanar da zanga-zanga da nufin gwada damuwarmu kan halin da kasarmu take ciki. Wasu daga cikin su na cikin halin ni 'ya su, wasu da raunuka a jikinsu. Idan zanga-zanga laifi ne, ya kamata a ce dimukuradiyya ma laifi ne a dokar Najeriya, tun da dimukuradiyya ce ta samar da zanga-zanga". 

Karin bayani: Najeriya: Zanga-zanga ta koma zubar da jini

Kotu na tuhumar masu zanga-zanga da laifuffuka 10 ciki har da cin amanar kasa
Kotu na tuhumar masu zanga-zanga da laifuffuka 10 ciki har da cin amanar kasaHoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Kotu ta cika makil da jama'a da suka zo sauraon shari'ar inda a Abuja aka gabatar da mutane 10 bisa laifuffuka shida da ake zarginsu da aikatawa. Sifeto janar na 'yan sandan Najeriya na zargin matasan da hada kai da wani dan kasar Birtaniya Andrew Wyne domin hargitsa Najeriya. 

Gwamnatin Najeriya ta sha kare matsayinta a kan zanga-zangar da aka gudanar. Alhaji Mohammed Idris da ke zama ministan yada labaru da wayar da kan jama'a ya ce: " Ba mu ga amfanin wannan zanga-zanga ba. Kullum aikin wanda ke shugabanci, shi ne ya jawo hankalin mutanen da yake shugabanta ga wasu abubuwa da shi yake gani, amma watakila su ba sa gani."

Karin bayani: Akwai darasi bayan zanga-zangar Najeriya?

Alkalin kotun daukaka kara ta Najeriya da ke Abuja ya sanya ranar 11 ga watan Staumba domin ci gaba da shari'ar tare da sauraren batun bayar da belin matasan da aka gabatar.