Gurfanar Bosco Ntaganda a gaban kotun ICC
February 10, 2014Talla
Ntaganda wanda ake kira da sunan Terminator wanda kuma shi ne babban kwamandan kungiyar FPLC, ana tuhumarsa da aikata laifukan fyade da kisan ƙare dangin da kuma kwasar ganima a gabashin Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kwango.
A yaƙin da aka yi tsakanin shekarun 2002 zuwa 2003 a yankin Ituri tsakanin 'yan ƙabilarsa ta Hema da na Lendu. Ƙungiyoyi masu zaman kansu sun ce yaƙin na gabashin Kwango ya yi sanadiyyar mutuwar mutane dubbu 60. A cikin watan Afrilu na shekarar bara ne dai Ntaganda ya miƙa kansa ga kotun ta ICC.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal