Guguwa ta yi barna a Indiya
May 3, 2019Talla
Hukumomi a kasar Indiya sun fara kwashe dubban mutane da ke kusa gabashin bakin ruwa a yankin arewa maso gabashin kasar sakamakon guguwa mai karfi da ta kunno, hukumar kula da yanayi ta ce ana sa ran guguwar da ke gudun kilomita 200 a sa guda za ta haddasa zabtarewar kasa a wasu sassan kasar. Guguwar Fani ta lalata gidaje da turakan lantarki da wayoyin sadarwa an kuma dakatar da sufurin jiragen kasa, hukumomi sun gargadi al'umma da su kauracewa yakunan da ke kusa da bakin ruwa don gudun ambaliya.