1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pakistan: Gomman mutane sun mutu a hatsarin jirgin kasa

June 7, 2021

A Pakistan a kalla mutum 30 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu mutum 100 suka jikkata a wani hatsarin jirgin kasa da ya auku a kudancin kasar.

https://p.dw.com/p/3uVuY
Pakistan Zugunglück
Hoto: Xinhua/imago images

Rahotani na nuna cewa hatsarin ya auku ne bayan da wasu jiragen kasa biyu dauke da fasinjojin kimanin 1000 suka yi taho mu gama da juna a Daharki dake arewacin lardin Sindh.

Tuni wasu ma'aikatan agaji a kauyukan da ke kusa da wurin suka fara aikin ceto wadanda suka jikkata tare da lalubo wasu da suka makale a cikin baraguzan jiragen.

Shugaban rundunar 'yan sandan yankin Umar Tufail ya ce tuni suka bukaci agajin manyan injina da su taimaka wajen kai wa wadanda suka makale dauki.

Hukumar tashar jiragen kasar ta Pakistan ta bada umurnin gudanar da bincike kan musababbin aukuwar hatsarin.

A Pakistan dai ana yawan samun hatsarin jiragen kasa, saboda zargin gwamnatin kasar da ake yi na kin zuba jari a wannan fannin.