1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Goita zai daina samun tallafin Bankin Duniya

Suleiman Babayo MAB
June 5, 2021

Bankin Duniya ya katse ba da kudin tafiyar da ayyuka a kasar Mali sakamakon sake juyin mulkin da sojoji suka yi bisa jagorancin Kanal Assimi Goita.

https://p.dw.com/p/3uSkW
Mali Oberst Assimi Goita, neuer Übergangspräsident
Hoto: AP Photo/picture alliance

Matakin Bankin na Duniya ya kara matsin lamba ga mahukuntan Mali bayan Faransa ta jingine aikin hadin gwiwa da sojojin kasar kan yaki da tsageru masu dauke da makamai.

Tuni jagoran juyin mulkin Kanar Assimi Goita ya nada Choguel Maiga a matsayin sabon firamnista. Ita ma kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS/CEDEAO ta dauki matakin dakatar da kasar ta Mali bayan juyin muliin da sojoji suka sake yi a karo na biyu cikin watanni tara.

Sai dasi magoya bayan gwamnatin mulkin sojan ta Mali sun yi gangamin nuna goyon baya a birnin Bamako fadar gwamnatin kasar a wannan Jumma'a da ta gabata.