Mexico: Gobara ta yi sanadiyyar rayuka
January 19, 2019Talla
Gobara ta ritsa da wani bututun mai da ya huje wanda ya yi sanadiyyar rayukan mutane 20 tare da raunata wasu gommai a Mexico.
Mazauna yankin sun yi yunkurin amfani da bokatai wajen dibar mai daga bututun, lokacin da wutar ta barke. Gwamnan jihar Hidalgo Omar Fayad ya fadawa manema labaru cewar, wajen mutane 54 suka samu raunuka a yayin da aka tabbatar da mutuwar wasu 20.
Shugaba Andres Lopez Obrador ya bayyana damuwa dangane da wannan hatsari da ya auku a Hidalgo ta shafinsa na Twitter, inda ya yi kira ga gwamnati da ta taimaka wa wadanda gobarar ta ritsa da su.