Bala'i
Gobara a asibiti da ke Indiya
December 17, 2018Talla
Wata gobara da ta tashi a wani asibitin gwamnatin da ke birnin Mumbai na kasar Indiya ta halaka kimanin mutane shida, yayin da wasu fiye da 130 suka samu raunika. 'yan sanda sun ce godabarar ta tashi daga hawa na hudu na asibitin mai hawa biyar, inda 'yan kwana-kwana da masu aikin ceto suka taimaka wajen dakile wutar da ta tashi.
Ana yawan samun tashin gobara a kasar ta Indiya inda ake zargin sakaci kan rashin daukar matakan kariya da suka dace.