Mutane 20 sun mutu a Pakistan
October 7, 2021Girkizar kasa mai karfin maki 5.7 ta halaka mutun 20 da sanyin safiyar wannan Alhamis a kudancin Pakistan. Wani kusa a ma'aikatar agajin gaggawan a lardin Balouchistan da lamarin ya auku Naseer Nasar, ya ce wasu daga cikin wadanda suka halaka har da mata da kananan yara.
A yanzu hakan ana ci gaba da kokarin kai daukin gaggawa ga wadanda hatsarin ya rutsa da su, sai dai rahotanni na cewa lamarin ya fi kamari ne a yankin Harnai da ke cikin tsaunuka, kana kuma rashin wadatattun hanyoyin da layukan sadarwa, na kara dagula al'amuran ceton.
Masu aiko da rahotanni sun ce an jiyo karar gigizar kasar har a lardin Quetta mai nisan kilomita 100 daga yankin. Ko a shekarar 2015 wata girgizar kasa mai karfin maki 7,5 ta yi sanadiyar salwantar ruyukan mutane 400 a lardunan da ke iyakokin Pakistan da Afghanistan.