Girgizar kasa ta kashe dubban mutane a Nepal
April 27, 2015A sakamakon bala'in girgizar kasar da ta kashe mutane da dama a kasar Nepal, tuni kasashen duniya sun fara kai daukin agajin gaggawa, da taimakon kayan barguna da injinan Jannareto da kuma jami'an lafiya, domin gaggauta samo bakin zaren, da kuma ceto wadanda ke da rai a wannan hadari da ya auku. Taimakon kasashen duniyar ya biyo bayan shelantawa da gwamnatin kasar ta Nepla ta yi, na neman agaji.
Wannan girgizar kasa mai karfin maki 7.9, wacce kawo yanzu hukumomi su ka tabbatar ta hallaka mutane fiye da dubu uku da dari bakwai (3700), yayin da wasu dubbai suka samu raunika, sannan kuma ga kananun girgiza a bangarorin babban birnin kasar Kathmandu, da hakan ake kyautata zaton shi ne ke janyo yawan katsewar wutar lantarki.
Cikin wani taron ganawa da manema labarai da sakataren gwamnatin kasar Chief Lila Mani Paudyal ya roki kasashen duniya wajen kai musu agaji.
Yanayin tausayawa da al'ummar kasar ke ciki a halin yanzu ya sanya hukumomin sauran kasashen duniya irin Faransa da, Indiya da, Koriya ta Kudu amsa kiran agazawa, inda Tarayyar Turai ke kan gaba a wannan fage, wajen ba da tallafin kudi kimanin Euro milyan uku, kamar yadda mai Magana da yawun hukumar Tarayyar Turai Natasha Bertaud ta bayyana a birnin Brussel na Belgiyam.
Kasar China ta shiga rukunin farko na kai dauki da irin kayayyakin da gwamnatin Nepal ta ambata.
Wannan girgizar kasa dai ita ce irin-ta ta biyu kuma wadda ta yi muni a tarihin kasar Nepal, tun shekarar 1934, inda aka yi girgizar da ta halaka mutane kimanin dubu takwas da dari biyar (8500), dubbai suka jikata a yayin da wasu mutanen 66 suka mutu a kan iyakar kasar da Indiya. Ana dai kyautata zaton samun bayani na karuwar yawan wadanda suka hallaka dalilin wannan annoba, domin har yanzu rahotanni sun ce masu aikin ceto, na tsaka da tone gine-ginen da suka rushe.