Girgizar kasa ta hallaka mutane a Mexico
September 8, 2017Talla
Lamarin dai ya fi kamari a jihar Chiapas da ke kudancin kasar kuma tuni jami'ai suka fara aiki na duba irin ta'adin da girgizar kasar ta yi. Ya zuwa yanzu dai mutum biyar ne suka rasu amma an ce adadin na iya karuwa. Masu aiki da rahotanni sun ce masana yanayi na tunanin girgizar kasar wadda ta kai maki takwas a mizanin da ake auna karfi girgizar kasa ka iya taimakawa wajen samun bullar mahaukaciyar igiyar ruwan nan ta Tsunami. Mutane da dama dai sun kauracewa matsugunansu kana kasashen da ke makotaka da inda abin ya faru ciki kuwa har da Costa Rica da Nicaragua da Honduras da Ecuador sun fara daukar matakai na kariya.