Gini ya rufta da mutane da dama a Indiya
September 27, 2013Rahotanni daga birnin Mumbai na kasar Indiya na cewar wani gini mai hawa biyar da ya rushe ya danne kimanin mutane saba'in da ke cikinsa.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito cewar a wannan Juma'ar ce ginin ya rushe kuma tuni masu bada agaji na gaggawa suka dukufa wajen zakulo mutanen da ke cikin baraguzan ginin da ya rushe.
Da ta ke tabbatar da faruwar wannan hadari, guda daga cikin jami'an gwamnati da ke yankin da abin ya faru Manisha Mahiskar ta ce ya zuwa yanzu an samu nasarar zakulo mutane bakwai da ransu.
A kwanakin baya ma dai an samu irin wannan ibtila'i a birnin na Mumbai inda kimanin mutane 74 suka rasu. Galibi dai ana alakanta faruwar wannan matsala da rashin ingancin ginin.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman