1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gidauniyar tallafawa harkar ilimi a Katsina

October 5, 2016

Wani matashi mai hannun baiwa ya kafa gidauniyar tallafa wa harkar ilimi inda yakan sayi babura ya ba iyaye don a rika yi musu acaba

https://p.dw.com/p/2Qtod
Nigeria Makoko schwimmende Schule in Lagos
Hoto: Reuters/A. Akinleye

Ganin irin halin da iilmi ya shiga na koma baya a yankin funtuwa da ke jihar Katsina ya sa wani matashi mai hannun baiwa ya kafa gidauniyar tallafa wa harkar ilmin inda yakan sai babura ya ba iyaye dan a rika yi masu acaba ana samar musu kudaden da zasu yi dawainiyar karatun yayansu.

Haka kuma yakan dinkawa marayu kayan kamaranta inda ya kashe kusan milliyan goma sha uku wajen hidimar ilimin.Ita dai wannan gidauniyar tana gudanar da tallafinta ga bangarorin ilimin yara marayu da ma iyaye marasa galihu.

Idris Danliman Funtuwa shi ne shugaban wannan gidauniya ya shaidawa DW cewa tada tallafi ga harkar ilmi ya zama wajibi ganin irin kalubalen da yake fuskanta

Ganin akwai wadansu iyaye da suna bukatar yayansu su rika zuwa makaranta amma babu halin hakan to ko gidauniyar takan kai daukinta garesu Danliman cewa yayi

Danliman daga nan sai yaja hankalin Al,umma dasu tallafama bangare ilmi dan cigaban kasa

Naji ta bakin wasu iyaye wadanda suka amfana da tallafin wannan gidauniya


Bada tallafi ga harkar ilimi na daya cikin abunda al,umma zasu dade su na amfani da shi ganin irin kololuwar daukakar da mai ilmi ka iya kaiwa.