Ghana ta samu ci gaba ta fuskar arzikin zinare
June 8, 2024Talla
Rahotannin da ke fitowa daga kasar Ghana, na nuna cewa kasar na samun ci gaba da fuskar arzikin Gwal wato Zinare, inda alkaluma ke nuna cewa ta samu karuwa da kashi 8.3% .
Hakan na nufin a shekarar da ta gabata Ghanar ta samu karin nauyin Zinare miliyan hudu, daga abin da hukumar kula da harkokin hakar albarkatun karkashin kasa ta nunar a jiya Juma'a.
Ci gaban da kasar ta Ghana ta samu a fannin ma'adinin dai, na da alaka ne sosai da abin da matsaikatan masu aikin hako zinaren suka yi.
Ana dai hasashen kasar ta iya samun karuwa a bana da akalla zinare mai nauyin miliyan 4.5 a ma'aunin ounce.