1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana ta sa haraji kan hada-hadar zamani

Abdul-raheem Hassan
March 29, 2022

Majalisar dokokin Ghana ta amince da sabon harajin hada-hadar kasuwanci da na’ura mai kwakwalwa wanda gwamnatin ke fatan samun dala miliyan 900 na kudaden shiga, sai dai matakin ya sha kakkausar suka daga 'yan adawa.

https://p.dw.com/p/49CKt
Ghana Accra | Kasuwa
Hoto: Christian Thompson/Anadolu Agency/picture alliance

Tsarin harajin da ake kira E-levy, zai gabatar da harajin kashi 1.5 kan hada-hadar kudade ta zamani, wanda gwamnatin Shugaba Nana Akufo-Addo ta ce zai taimaka wajen magance matsalolin rashin aikin yi zuwa ga dimbin basussukan da kasar ke fama da su.

Sai dai ga da yawa daga cikin ‘yan Ghana na cewa harajin na sake zama wani nauyi a gare su, domin tuni suka fara kokawa da tsadar rayuwa sakamakon hauhawar farashin man fetur sakamakon rikicin Ukraine.

‘Yan majalisar sun amince da dokar ne bayan ‘yan tsirarun ‘yan adawa sun fice daga muhawarar. A baya-bayan na kasar Ghana ta sake bude iyakokinta na kasa da na teku bayan shekaru biyu a rufe saboda korona, ta kuma dage wasu takunkumin hana yaduwar cutar coronavirus a kokarinta na bunkasa tattalin arzikinta.

Shugaban kasar da ministocinsa sun yanke albashinsu kashi 30 cikin 100, tare da wasu matakan da suke fatan za su taimaka wajen samar da dala miliyan 400 a asusun gwamnati.