Ghana: Cin hanci a ciyar da dalibai abinci
November 19, 2024Akalla buhunan shinkafa 22,000 ne ake zargin an ciyar da daliban makarantun sakandaren da aka rarraba bayan da aka shigo da shinkar daga kasar India. Samuel Okudjeto Ablakwa,dan majalisar dokokin Ghana kuma jigo a bangaren adawa ya kwatanta al'amarin tamkar wata manakisar hukumomin gwamnati dan aikata laifi da kuma jefa rayuwar dubban daliban da iyaye suka kai makarantu cikin garari. Iyaye wadanda lamarin ya rutsa da yayansu sun zanta da DW.
Yanzu 'ya'yanmu na fama da ciwon ciki sakamakon wannan abinci, kuma idan aka kyale ba a yi komai ba aka yi shuru akan wannan maganar, za mu yi zanga-zanga. Muna cikin bacin rai akan shinkafar da ta lalace aka dafa wa dalibai har ma yawanci na kwance babu lafiya. Yanzu dai mun bai wa gwamnati wa'adin sati daya wajibi ne a hukunta wadanda ke da alhakin wannan abu a gaban hukuma.
Jama'a na mamaki ta yaya aka yi sakacin shigo da gurbatacciyar shinkafar? ta yaya kuma za'a kauce wa aukuwar hakan a nan gaba? Mai sharhi akan al'amuran yau da kullum Isa Jibril Abbas Mairago yayi tsokaci.
Laifi dai ya rataya ne a wuyan gwamnati da kuma hukumar kula da ingancin kayan abinci, lura da cewa gwamnati ta kawar da kai da rashin kula na wadan nan kayayyakin abinci, da kuma kin bai wa hukuma mai iko da ta gudanarda aikinta yadda ya kamata.
Ma'aikatar ilimi ta Ghana ta ce tarar da hukumar FDA ta ci kampanin ya danganci sake buhunan shinkafar ne ba da sahalewar hukumar FDA ba, amma ba akan ingancin abincin ba.
Sadia Abubakar yar rajin kare hakkin yara da mata ta yi tsokaci akan yanayin abincin ma da ake bai wa dalibai a makarantun kasar dake bukatar sauyi.