Gawar Mandela ta kama hanyar kushewa
December 14, 2013A wannan Asabar rundunar sojan ƙasar Afirka ta Kudu ta miƙa gawar tsohon Shugaba Nelson Mandela wa jam'iyyar ANC mai mulki na wani lokaci, domin mambobin jam'iyyar su yi bankwana na ƙarshe wa marigayin tsohon jagoran gwagwarmaya da mulkin nuna wariyar launin fata. Wani lokacin a yau bayan kammala wannan girmamawa da ake yi yanzu haka a birnin Pretoria, wani jirgin sama na soja zai ɗauki gawar Marigayi Mandela zuwa kusa da garin Qunu inda za a binne shi gobe Lahadi. Yanzu haka sojoji da sauran jami'an tsaro sun yi wa garin na Qunu tsinke, inda za a yi jana'izar Mandela.
Gwamnatin ƙasar ta Afirka ta Kudu ta ce kimanin mutane dubu 100,000 suka samu damar yi wa gawar Mandela bankwana cikin kwanaki da suka gabata, lokacin da aka shinfida gawar a wani ginin gwamnati.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Abdourahamane Hassane