Gasar cin kofin Turai
June 21, 2021Su ma dai kasashen Beljiyam da Neatherlands sun kusa tsira domin dukansu suna saman tebur a rukunin B da C da maki shida-shida. Sai dai kasashen Faransa da Potugal da Jamus a ke a rukunin F, har yanzu ba su san matsayinsu ba, domin kuwa Faransa da ke saman tebur maki hudu ne da ita kacal, abin da ke nuni da cewa maki daya ne tsakninsu da kasashen Jamus da Potugal da dukansu ke da maki uku-uku.
Hakan dai na nuni da cewa duka kasashen uku tilas su kai bantansu a wasan da za su fafata karo na uku kuma na karshe a zagayen farko na gasar. A ranar Laraba mai zuwa ne dai kasar Potugal za ta kece raini da takwararta da Faransa yayin da Jamus za ta fafata da Hangarai.
Ko ma dai ya ake ciki, kasashen na Jamus da potugal da ma ita Faransan na da damar tsallaka wa zagaye na biyu, in har aka yi la'akari da tsarin nan na wanda ya fi taka rawa a mataki na uku a kowanne rukuni na da damar tsallaka wa zuwa zagaye na biyun.
Su kuwa kasashen Turkiyya a rukunin A da Denmak a rukunin B da Macedorniya a rukunin C da Scottland a rukunin D da Poland a rukunin E da kuma Hangarai a rukunin F sun gaza kai bantensu a wannan gasa.