Ganawar Mandela da Bush
May 18, 2005Tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu Nelson Mandela ya tattauna da shugaba george W Bush na Amurka dangane da yiyuwan rage basussuka da ake bin kasashe masu tasowa da matalauta.
Tsohon shugaban na Afrika ta kudu wanda ya taba karbar lambar yabo na zaman lafiya ta nobel,yayi wannan tattaunawan ne da shugaban Amurka a fadar gwamnati ta white house dake birnin washinton,a yayin ziyarar daya kai a Amurkan.
A wannan tattaunawa tasu dai kamar yadda jamiai sukayi nuni dashi basu tabo batun yakin Iraki ba,wanda ke zama wani babban batu na rashin jituwa tsakanin mutanen biyu.Mandela dai yana daya daga cikin mutanen da sukayi adawa da harin da Amurka tayiwa jagiranci a Iraki a shekara ta 2003,to sai dai gabannin wannan ganawar tasu ya bayyana cewa wannan rashin jituwa ne tsakanin abokai.
Kakakin fadar gwamnatin Amurka Scott McClellan yace shugaba Bush yayi maraba da ziyaran Mandela a White House,ziyarar data samarda kyakkyawan fahinta tsakaninsu.
Shugabannin biyu dai sun tattauna matuka gaya kan yadda zaa shawo kan yaduwar cutar AIDs a nahiyar Afrika da kuma yiwuwan yafe wasu daga cikin basussuka da ake bin kasashen.
McClellan yace shugaba Bush yayi alkawarin taimakawa wajen yafe wasu basussukan kasashen Afrika tare da gabatar da batun a gaban taron kungiyar kasashe takwas masu arzikin masanaantu a duniya watau G8,taron dazai gudana a watan Yuli a Scotland.
Kakakin White House yace ko kadan shugabannin biyu basu tabo batun Iraki ba,sai dai Bush ya yaba da irin rawa da Mandela ke takawa a matsayin shugaba kuma uba.
A jawabin dayayi a birnin Washinton a ranar Litinin Mandela ya yi nuni dacewa yayi adawa da yakin da akayi a Iraki,a karkashin abunda Bush ya kira yayata yancin walwala,ta kowace hanya,musamman a Irakin.
Yace yana marawa yunkurin Shugaban na Amurka na samarda yancin walwala,amma ko kadan bai amince da anfani da karfin soji wajen cimma wannan buri ba ,kamar yadda aka aiwatar a Iraki.Yace akan samu irin wannan rashin jituwa tsakanin abokanai.
Mandela yace yancin walwala bashi da muhimmanci wa mutumin dake bakin mutuwa daga cututtuka da zaa iya maganta masa ko kuma kareshi daga kamu dasu,amma akayi watsi da hakan.
Mandela yayi amfani da wannan ziyara wajen kira ga Amurka da sauran kasashe masu cigaban masanaantu dasu taimakawa Afrika kan matsaloli da suka maida hankali wajen warwaresu da suka hadar da talauci da basussuka.
Duk dacewa yayi ritaya da harkoki na gwamnati,Mandela mai shekaru 87 da haihuwa,mutumin daya kasance a gidan yari na tsawon shekaru 27 akarkashin mulkin mallaka na turawa har ya zuwa samun yancin democradiyya a shekara ta 1994,na samun gudanar da ziyarce ziyarcensa ne tare da agajin mataimaka,saboda yanzu bashi da karfin yin haka da kansa.