1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gambiya za ta fice daga kotun ICC

October 31, 2016

Kasashen Afirka da dama na ficewa daga kotun kasa da kasa mai shari'ar masu manyan laifuka ta ICC da ke da matsuguninta a birnin Hague na kasar Netherlanda.

https://p.dw.com/p/2RwFo
Yahya Jammeh
Hoto: AP

A sharhin data rubuta kan wannan batu jaridar Süddeutsche Zeitung cewa ta yi, bayan kasashen Afirka da Kudu da Burundi, Gambiya ita ma ta bi sahu na ayyana mafurta na ficewa daga kotun kasa da kasar ta ICC. Da yammacin ranar Talata ce dai, ministan yada labaru na Sheriff Bojan ya gabatar da wannan sanarwa ta gidan talabijin na Gambiya. Sanarwa ta yi nuni dacewar, kotun tamkar an kirkirota ne saboda kasashen Afirka da shugabanninsu, wanda za'a iya fassarashi da cin mutunci ga ilahirin nahiyar.

Takwas daga cikin shari'a tara da a yanzu haka ke gaban kotun dai sun shafi kasashen Afirka ne. Ministan yada labarun na Gambiya Bojang ya ce, tun kafuwar kotun shari'ar masu manyan laifukan ta kasa da kasa, shugabannin kasashen yammaci na Turai sun aikata manyan laifuka na yaki akalla 30, ba tare da an gurfanr da su ba...inda ya yi nuni da yake yaken Afganistan da Iraki da da Libiya da kuma uwa uba Siriya. Shi ma dai shugaban Yuganda Yoweri Museveni a ranar Laraba ya bayyana kotun ta ICC da kasancewa wurin shiririta.

Sai dai ga babbar mai gabatar da kara na kotun mai matsuguni a birnin Hague watau Fatou Bensouda, ficewar Gambiya daga kotun babban koma baya ne a gareta. Domin ita 'yar asalin wannan kasace ta yammacin Afirka. Lokacin da shugaba Yahya Jammeh ya hau karagar mulki a shekara ta 1994, Bensouda ta kasance mai bashi shawara. Ta kasance ministar shari'a tsakanin 1998 zuwa 2000. Yanzu haka dai kasar ta koma mulki irin na kama karya, inda ake cigaba da take hakkin jama'a, kana mafi yawa daga al'ummarta ke yin kasadar tafiyar neman tudun mun tsira ta tekun Meditranian.

Kenia Anschlag in der Stadt Mandera
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tsokaci ta yi game da harin da aka kai a Kenya. A karshin labarin da ta rubuta mai taken "hari a yankin gabashin Kenya" jaridar ta ci gaba dacewa, da sanyin safiyar ranar Talata ce aka kai hari a wani Hotel a garin Mandera dake yankin Arewa maso Gabashin kasar ta Kenya. Akalla mutane 12 suka rasa rayukansu.

Da misalin karfe uku da rabi na asubahin ne dai aka ji fashewar wani abu mai kama da bam a wani bangare na ginin hotel Bishaaro. Akwai dai sabani dangane da adadin mutanen da ke hotel din a lokacin wannan harin, kasancewar wasu sun gamu da ajalinsu ne a yayin da suke barci.

Sanannen abu ne dai cewar, kungiyar al Shabaab ta Somalia ce keda alhakin kai wannan harin. Mandera dai gari ne da ke kan Kenya da Somaliya. Hare-hare sau biyu cikin watanni shida da suka gabata ya yi sanadiyyar rayukan mutane shida a wannan gari.

Mali UN Angriff ARCHIV
Hoto: Getty Images/AFP/S. Ag Anara

A yanzu haka dai Jamus na kokarin fadada ayyukan dakarunta a yankin arewacin Mali mai hadari. Da take tsokaci a kan wannan batu, jaridar Süddeutsche Zeitung cewa ta yi  , ministan kula da harkokin ketare  Frank-Walter Steinmeier na jam'iyyar SPD da ministar tsar Ursula von der Leyen ta CDU, sun amince da tura jiragen kirar saukar ungulu nakula da marasa lafiya da na yaki zuwa kasar Mali da ke yammacin Afirka, a karkashin shirin nan na hadakar sojojin MDD na MINUSMA.))