Shugaba Ali Bongo ya tsige mataimakinsa
May 22, 2019Talla
Fadar shugaban kasar ta Gabon ta sanar da daukar wannan mataki ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a daren jiya Talata. Sai dai ya zuwa yanzu a hakumance fadar ba ta bayyana wasu dalillan Shugaba Ali Bongo na daukar wannan mataki ba.
Amma dai matakin tsige mataimakin shugaban kasar na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan kasar da dama ke ta sa kira ga shugaban kasa na ya sauke mataimakin nasa da ministan muhalli da kula da itatuwan kurmin na kasar wadanda ake zargi da hannu a wata badakalar fataucin itatuwa masu daraja wadanda dokar kasar ta haramta kisansu.