1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gabon: Kame-kamen 'yan adawa masu zanga-zanga

Salissou Boukari
August 27, 2017

Hukumomi a Gabon sun tabbatar da kame wasu 'yan adawar kasar guda 11 bayan wata zanga-zanga da suka yi ta goyon bayan babban dan adawan nan na kasar Jean Ping da ke ikirarin cewa shi ne ya ci zaben kasar.

https://p.dw.com/p/2ivoq
Gabon Studenten Proteste in Libreville Archiv 18.04.2012
Masu zanga-zanga a kasar GabonHoto: Tiphaine Saint-Criq/AFP/Getty Images

A ranar Juma'a da ta gabata ne dai 'yan adawar kasar ta Gabon masu goyon bayan Jean Ping suka gudanar da zanga-zanga a wasu sassan kasar. A birnin Port-Gentil ma dai an kama mutane uku daga cikin masu zanga-zangar wanda hakan ya kai adadin mutane 11 na wadanda aka kaman. Hukumomin kasar sun ce an yi zanga-zangar ne ba bisa ka'ida ba, batun da 'yan adawan suka ce ba haka yake ba, domin kuwa sun ajiye takardar neman izini tun a ranar Laraba ba tare da samun amsa ba.

Ta shafukan sada zumunta ne dai, ofishin ministan cikin gidan kasar ta Gabon ya ce dukannin wadanda aka kama za a gurfanar da su ne a gaban shari'a. Zanga-zangar dai ta gudana ne kwanaki biyu kacal kafin ranar cikon shekara guda da zaben da suka ce basu yarda da shi ba, wanda shugaban kasar mai ci Ali Bongo Odimba ya sake lashe wa, wanda a wannan Lahadin ce 27 ga watan Augusta zaben ya cika shekara daya daidai.