1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gabon: Jean Ping ya yi ikirarin lashe zabe

Ahmed SalisuAugust 28, 2016

Madugun 'yan adawar Gabon da ya yi takarar shugaban kasar da shugaba Ali Bongo ya yi ikirarin lashe zaben da aka gudanar a kasar a ranar Asabar da ta gabata.

https://p.dw.com/p/1JrOF
Gipfel Afrikanische Union Addis Abeba
Hoto: Reuters

Jean Ping ya shaida hakan ne lokacin da ya yi wani jawabi ga darururwa magoya bayansa a Liberaville wanda shi ne babban birnin kasar, inda ya ke cewar ya na jira ne shugaba Bongo ya kira shi don taya shi murna tare da shaida masa cewar ya amince da shan kaye.

To sai dai Shugaba Bongo din ya ce ya yi wuri a ce wani ya yi ikirarin samun nasara, inda a hannu guda ya ce zai tsumayi fitar kamallalen sakamakon zaben kafin cewa wani abu. A ranar Talatar da ke tafe ce da misalin karfe 4 agogon GMT cikakken sakamakon zaben zai fita kamar yadda ministan cikin gidan Gabon din ya shaida, inda ya kara da cewar duk wanda ya bayyana cewar ya yi nasarar kafin wannan lokaci to ya sabawa doka.