Gabon: Horo domin magance zaman banza
February 8, 2017Willy-Conrad Asseko-Allogo mai shekaru 32 a duniya ya samu nasarar kafa kamfanin sifiri da ke samar da hanyar dogaro da kai. Matashi ne mai hazaka da ke jagorantar kungiyoyi da dama a Gabon a yanzu ya bude fagen wasan kwallon kwando. Wannan ya sa Asseko ke ganin matan Gabon ka iya taka wani matsayi na rayuwa a kungiyar ko baya ga wasan, yana mai cewa:
"Kwallon kwando zai taimaka wa matasa fadawa cikin matasaloli. Saboda muna da damar tattaunawa da su da lura da yanayinsu, tanan za mu iya dafa musu a duk abin da suka sa a gaba. Kazalika akwai damar tallafa wa mata."
Ko da ya ke dai Asseko wanda shekaru bakwai kenan yanzu da kasuwancinsa ke samun nasara, ya yi wa kasar Gabon wasan kwallon kwando a matakin kasa, to amma bayan kammala karatunsa a Jamus, ya yanke shawarar koma wa kasarsa ta haihuwa inda ya bude harkar sifiri tun yana da shekaru 24. Amma duk da haka Asseko na ganin akwai rawar da zai taka wajen kawo sauyi a rayuwar matasa musamman wajen amfani da wasanni domin cimma tsarin shugabanci da Ilimi da ma dora al'umma a harkokin kasuwanci. Ko da ya ke dai Gabon na takama da arzikin mai to amma matasa na fama da rashin aikin yi, wannan ya sa Asseko tunanin koma wa gida bayan kammala karatunsa, inda a yanzu ya ke bai wa matasa da dama horo na samun aikin yi. A yanzu ma dai Asseko na aiki kan wani manhajar wayar salula da za su sawa suna Oyeni- tare da abokanan huldarsa da suke sa ran samar da gagarumar dama a nahiyar Afirka baki daya. Charlene Mboumba mai yin kitso ce na zamani da ke cikin wadanda ke hada gwiwa da Asseko dan bunkasa cibiyoyin tallafa wa masu tasowa a Gabon, ta ce:
"Yana taimaka wa, yana karfafa gwiwa ta yadda za ka yi tsimi da tanadi. Saboda haka ya tallafamin wajen rubanya kaswuancina."