Gabon: Alain-Claude Bilie-By-Nze ya zama sabon firaminista
January 9, 2023Talla
Shugaba Ali Bongo Ondimba na kasar Gabio ya nada Alain-Claude Bilie-By-Nze a matsayin sabon firaministan kasar a wannan Litini, inda zai maye gurbin Rose Christiane Ossouka Raponda, da za ta kasance mataimakiyar shugaban kasa.
Fadar shugaban kasar ce ta sanar da haka, a daidai lokacin da masu adawa da gwamnatin Ali Bongo ke cigaba da korafi kan rashin iya mulki.
Bilie-By-Nze, mai shekaru 55 a duniya, ya taba rike manyan mukamai a cikin gwamnatin Bongo Ondimba tun a shekarar 2006, ciki har da ministan makamashi da mukamin mataimakin firaminista