1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gabatar da Ntaganda a gaban kotun ICC

February 10, 2014

Ana zargin tsohon madugun 'yan tawayen kasar Kongo ne da laifukan yaki da suka hadar da take hakkin jama'a da cin zarafi, a yakin da ya gudana a yankin gabashin kasar.

https://p.dw.com/p/1B66t
Hoto: Reuters

Wannan dai na zama wani mataki na kaddamar da shari'ar ta Bosco Naganda a wannan kotu ta kasa da kasa da ke birnin The Hague, amma a hukumance zai dauki tsawon lokaci kafin fara sauraron shari'ar ita kanta.

Ana dai zargin tsohon madugun 'yan tawayen ne da laifuffuka da ya ke da hannu a baya da irin ta'asa da suka tabka tsakanin shekarun 2002 zuwa 2003, a karkashin shugaban kungiyar soji masu fafutu ta kongo Thomas Lubanga, wanda tuni aka zartar da hukunci akansa bisa ga samunsa da laifuffukan da suka hadar da cin zarafin jama'a ta hanyar lalata da azabtarwa da sanya yara kanana aikin soji da dibar ganima da kuma kisan gilla.

Kongo Armee sucht nach Milizenchef Bosco Ntaganda
Sojojin KongoHoto: dapd

A ranar 18 ga watan Maris ne dai Ntaganta ya yi wata bayyanar ban mamaki a ofishin jakadancin Ruanda, inda daga nan ne aka mika shi ga kotun kasa da kasa da ke birnin na Hague. Hakan dai na tabbatar da kawo karshen ayyukan tarzoma daya jima yana aiwatarwa a kongo. Na baya bayannan shine irin ta'asar da suka yi ta tabkawa a cikin kungiyar sojin saka na M23, wadanda suka yi fadan cimma kwace wasu yankunan arewacin Kivu a shekara ta 2012.

Kwararriya kan kasar ta kongo a Kungiyar kare hakkin jama'a ta Human rights Watch Ida Sawyer ta shaidawa DW cewar, Nataganda ya taka muhimmiyar rawa a rikicin kungiyar M23:

" Lokacin da kungiyar sojojin tawaye ta M23 suka fara fada a watan Afrilun 2012, ba boyayyen abu ba ne irin rawa da Ntaganda ya taka tun kafuwar wannan kungiya, zuwa ga zama shugabanta, sai suka nada Sultani Makenga a matsayin shugaban kungiyar a baynar jama'a , wanda hakan ba zai kasa nasaba da sammacin kama Ntaganda ta kotun kasa da kasa ta ICC ta yi ba, saboda gudun bata sunan kungiyar ".

Sakamakon fadar madafar iko a cikin kungiyar mayakan tawayen ne, aka samu ballewar wata kungiyar a karkashin Makenga, inda rikici ya sanya da yawa daga cikinsu suka tsere zuwa kasar Ruanda, kazalika Ntaganda.

Bosco Ntaganda Prozess ICC Den Haag 10.01.2014 Bensouda
Babbar mai gurfanar da kara Fatou BensoudaHoto: Reuters

Bayyanarsa a offishin jakadancin kasar Amurka, ba zai kasa nasaba da gudun kada a kashe shi ba ne, acewar Sawyer. Abunda ke nuni da cewar, yana shakkun samun mafaka har a kasar ta haihuwa. Ana masa kallon daya daga cikin tsoffin mukarraban shugaba Paul Kagame na Rwanda.

A cewar Martin Doevenspeck manazarci a birnin Bayreut da ke tarayyar Jamus dai " Bosco Ntaganda ya kasance haifaffen kasar Rwanda kuma dan tawayen kabilar tutsi ne, wadanda suka jima da kasancewa cikin rikicin na kongo, kuma suka jima suna fada a yankin gabashin kasar".

An haifi Bosco Ntaganta a shekara ta 1973, inda ya tun yana yaro ya tsere daga Rwanda zuwa Kongo, sakamakon mamaye da 'yan kabilar hutu suka yi musu, kamar yadda Paul Kagame ya tsere zuwa kasar Uganda.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Saleh Umar Saleh