Firaministan Libiya ya tsallake rijiya da baya
February 10, 2022Da safiyar wannan Alhamis din ne rahotanni suka tabbatar da kai wa Firaminista Abdulhamid al-Dbeibah hari da wasu 'yan bindiga suka yi. Masu aiko da rahoranni sun ce an kai masa harin ne a lokacin da yake kan hanyarsa ta koma gida, sai dai an yi sa'a ya tsira da ransa.
Maharan da aka bayyana danyen aikin da suka aikata a matsayin wani shiryeyyen lamari ne da ke nufin halaka Firaministan na Libiya, sun tsere nan take inda jami'an tsaro suka bazu domin zakulo su.
Yunkurin halaka Firamninstan na Libiya dai na iya dagula siyasar kasar, bayan sanarwar da ya yi na cewa zai yi watsi da zaben da aka shirya yi a ranar Alhamis domin samun wanda zai gaje shi. A shekara ta 2011 ne dai Libiyar ta fada cikin rigima, bayan juyin juya halin da ya kawo karshen gwamnatin marigayi Muamar Gaddafi.