1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Netanyahu na ziyarar aiki a Jamus

Kersten Knipp SB
June 4, 2018

Ziyarar na zama ta zuwa kasar da ke da dangantaka ta musamman da Isra'ila bisa fannoni daban daban. Dangantakar kasashen biyu ta kasance ta kut da kut tsawon shekaru da dama.

https://p.dw.com/p/2yvBB
Berlin Deutsch-Israelische Regierungskonsultationen Netanjahu Merkel
Hoto: picture-alliance/dpa/B. von Jutrczenka

Dangantaka tsakanin kasashen biyu tana da wata irin sarkakiya musamman sakamakon kisan Yahudawa miliyan shida da 'yan Nazi na Jamus suka aikata a lokacin yaki dauniya na biyu.

Duk da wannan batu dangantaka tsakanin Jamus da Isra'ila ta fara karfafa tun daga shekarar 1965 lokacin da gwamnatin Jamus ta kulla hulda ta diflomasiya da Isra'ila.

Deutschland Benjamin Netanjahu in Berlin
Firaministan Israila Benjamin NetanyahuHoto: Getty Images/C. Koall

A nasa bangaren Firaminista David Ben Gurion na Isra'ila ya nuna sasantawa a gaban komai. Shi dai firamnistan na farko ya nuna fahimta ga Jamus. Duk da yake sau biyu Ben Gurion ya gana da tsohon shugaban gwamnatin Jamus marigayi Konrad Adenauer a 1960 da 1966 amma sun zama tamkar abokai.

Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas ga abin da yake cewa gabanin ziyarar da ya kai zuwa Isra'ila cikin wannan shekara ta 2018:

"Na yi imanin mun amince da kusan daukacin manufofin sai dai hanyar aiwatarwa akwai bangabanci. Amma Jamus tana bangaren Isra'ila koyaushe."

Kisan da 'yan Nazi na Jamus suka yi wa milyoyin Yahudawa lokacin yakin duniya na biyu batu ne muhimmi amma bai zama ginshikin da ya rufe ido ba, kamar yadda dan jarida Michael Wolfsohn mai ruwa biyu, Jamus da Irsa'ila ke cewa

"Za mu iya gyara haka domin Isra'ila za ta iya wanzuwa ba tare da kisan kare dangi da aka yi wa Yahudawa ba. Kuma da Yahudawa milyan 6 sun tsira da ransu."

Deutschland Berlin PK Bundeskanzlerin Merkel mit Premierminister Benjamin Netanjahu
Angela Merkel da Benjamin NetanyahuHoto: Reuters/F. Bensch

Ita kanta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ga abin da ta shaida wa majalisar dokokin Isra'ila a shekara ta 2008 lokacin wata ziyara cewa:

"Kowace gwamnatin tarayya da shugabannin gwamnati da suka gabace ni sun jaddada kudirin Jamus kan daukar nauyin tarihi bisa tabbatar  tsaron Isra'ila."

Jamus da Isra'ila sun amince da abubuwa da dama, amma akwai rudani kan gina sabbin matsunan Yahudawa. Sai dai a cewar Peter Lintl masanin kan Isra'ila a wata gidauniya ta birnin Berlin na Jamus, yana ganin kowa ya saka kansa a yanayin Isra'ila zai fahimanci abin da ke faruwa:

"A daya bangare gaskiya ce. Ina tunanin mafi yawan kasashe Turai yana da matukar wuya su yi tunanin zama a yanayin Isra'ila. Wani tunanin shi ne yadda Yahudawa da Falasdinawa ke zaman doya da manja fiye da shekaru 100."

Peter Lintl ya kara da cewa wani karin abu shi ne har yanzu akwai kafofin yada labarai masu tababa kan sahihancin kafa kasar Isra'ila. Haka da rashin tabbas da ake ciki ya kara nuna babu yadda za a yi Turawa su yi tunanin zama cikin irin wannan yanayi.