1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Sabon shugaban gwamnatin Libiya ya isa Tripoli

Abdoulaye Mamane Amadou MAB
May 17, 2022

Rikici ya barke tsakanin mayakan sa kai a birnin Tripoli bayan da Fathi Bachagha sabon firaminitan Libiya da majalisar dokokin kasar ta nada ya je birnin Tripoli a wannan Talata.

https://p.dw.com/p/4BOUc
Libyen | Premierminister Fathi Bashagha
Hoto: Jihed Abidellaoui/REUTERS

Sabon Firaminita Fathi Bachagha da ke samun cikakken goyon bayan majalisar shu'ra ta gabashin kasar Libiya ya shiga babban birnin kasar ne tare da rakiyar wasu ministoci don fara aiki. Jim kadan bayan da aka bayyana shigar tawagar, rikici ya barke tsakanin mayakan sa kai da ke goyon bayan bangaren gwamnatin da na Firaminista Abdelhamid Dbeibah, da yanzu haka ke rike da maadafan iko.

Duk da turabukin da ya samu na zartar da harkokin mulki a Libiya, Fathi Bachagha ya kasa tafiyar da aikin gwamnati bisa kememen da hamshakin dan kasuwa kuma firaminista Abdelhamid Dbeibah ya yi na bayar da kai bori ya hau, bayan da majalisar ta shu'ra ta hakikance cewa ya kammala wa'adinsa na mulki.