Fargabar yunwa a yammacin Afirka
August 11, 2014Talla
Rahotanni sun bayyana cewa killacewar da aka yi wa yankunan da suke fama da masifar annobar cutar ta Ebola da kuma takaita zirga-zirga domin rage yaduwarta, ya janyo karancin abinci da matsalar ababen hawa da kuma tsadar kayayyakin masarufi.
Tuni dai matsalar karancin abincin ta shafi kasar Laberiya tun bayan da ta takaita zirga-zirgar jama'a daga arewacin kasar da annobar ta fi kamari zuwa Monrovia babban birnin kasar. Shima da yake bayani kan wannan sabuwar matsalar Joseph Kelfalah da ke zaman magajin garin Kenema na kasar Saliyo ya ce suna daukar matakai sai dai ya tabbatar da cewa akwai matsalar hauhawar farashin kayan abinci.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Suleiman Babayo