Fargabar tsanantar annobar cutar Ebola
September 3, 2014Dr. Joanne Liu da ke zaman shugabar kungiyar Medicines sans Frontiers ta ce alamu na nuna cewar hukumomin kiwon lafiya da kasashe na neman gazawa a yakin da ake da cutar, inda ta kara da cewar a yammacin Afirka ana samun karuwar wanda ke kamuwa da cutar da ma wanda cutar ta hallaka yayin da jami'an kiwon lafiya da ke jinyar masu cutar su ma ke kamuwa da ita kuma da damansu ke rasuwa wanda hakan ya sanya wasu jami'an na kiwon lafiya tserewa daga bakin aiki, lamarin da ya sanya ake barin masu wannan larura cikin wani hali.
Cutar Ebola dai yanzu haka ta yi sanadin rasuwar mutane kimanin dubu da dari biyar a Gini da Liberiya da Saliyo da kuma Najeriya wadda ke zaman kasa ta baya-bayan nan a yammacin Afirka da cutar ta bulla.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu