Fargabar kasa cimma muradin makamashi.
April 3, 2017Bankin Duniya ya bayyana fargabarsa a game da yiwuwar kasa cimma muradin da duniya ta sanya a gabanata na samar da makamashin lantarki ga ko wani dan Adam da kuma bunkasa hanyoyin samar da tsaftaccen makamashi nan zuwa shekara ta 2030. Bankin Duniyar ya bayyana hakan ne a cikin wani rahoto da ya wallafa a wannan Litinin.
A cikin wata sanarwa da ta fitar kan wannan batu, wakiliyar sashen kula da harakokin makamashi a Majalisar Dinkin Duniya Rachel Kyte ta gargadi shugabannin kasashen duniya da su kara azama wajen saka wadatattun kudade a fannin samar da makamashi domin ganin an cimma wannan buri nan zuwa shekara ta 2030.
Rahoton Bankin Duniyar ya ce a shekara ta 2014 akwai sauran mutane sama da miliyan dubu dari da ba su mallaki makamashi ba a duniya baki daya. Sai dai rahoton ya ce an samu ci gaba a fannin sama da makamashin a wasu kasashe kamar Afganistan, Kambodiya, Kenya, Uganda da Ruwanda.