1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sababbin rahotanni na bullar cutar Ebola a Afirka

Lateefa Mustapha Ja'afarFebruary 26, 2015

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta cean samu sababbin rahotanni na bullar cutar Ebola mai saurin kisa har 99 a kasashen Guinea da Laberiya da kuma Saliyo.

https://p.dw.com/p/1Ei2n
Hoto: Getty Images/J. Moore

A rahotonta da ta saba fitarwa duk mako, hukumar ta WHO ta ce cikin wannan mako ne aka samu rahoton bullar cutar ta Ebola, inda kasar Saliyo ke da mutane 63 cikin 99 da aka tabbatar suna dauke da kwayar cutar yayin da Guinea ke da mutane 35 kana Laberiya kuma na da mutum guda kadai. Hukumar ta ce samun sabon rahoto na yaduwar cutar a yanzu cikin kasashen uku, na nuni da cewa an samu nakasu a kokarin yakin da ake da Ebolan idan aka yi la'akari da karancin masu dauke da ita da aka samu a watannin Disambar bara da kuma Janairun wannan shekara da muke ciki ta 2015. Tun bayan bullar cutar dai sama da mutane 9,500 ne cutar Ebolan ta lakume rayukansu a yankin yammacin Afirka.