Dokar takaita zirga-zirga a Saliyo
June 13, 2015Koroma ya sanar da cewa dokar ta shafi yankin arewa maso yammacin kasar ta Saliyo, inda ya ce 'yan kasuwa ka iya ci gaba da harkokin kasuwancinsu in har za su kiyaye ka'idojin rigakafin cutar ta Ebola da suka hadar da tan-tance yanayin zafin jiki na ma'aikatansu da kuma masu sayan kaya. Shugaba Koroma ya kara da cewa:
"Dokar takaita zirga-zirgar da sojoji za su tabbatar da ganin an yi amfani da ita za ta kai tsahon makonni uku. Duk wanda ya saba wannan doka za a hukunta shi nan take. Za a rinka bude shaguna da ga karfe shida na safe zuwa karfe tara na dare daga Litinin zuwa Asabar. Gidajen sayar da abinci kuwa za su rinka budewa daga karfe shida na safe zuwa 10 na dare a ranakun Litinin zuwa Lahadi."
Annobar cutar Ebola dai ta hallaka mutane sama da 11,000 a tsahon watannin 18 a yankin yammacin Afirka.