SiyasaTurai
Faransa ta haramta sayar da ruwan roba mai guba na Olympics
July 20, 2024Talla
Faransa ta ba da umarnin janye wani ruwan sha na roba na kananan yara daga kasuwannin kasar, wanda aka yi shi na musamman don gasar Olympics, da za a gudanar a birnin Paris, sakamakon samun sinadari mai guba a mazubin.
karin bayani:'Yan damben wrestling na Rasha za su kauracewa Olympics na bana
Hukumar kula da ingancin abinci ta kasar ta ce sinadarin Bisphenol A da aka yi robar na da illa ga kwayoyin halittar bil'adama, da ke haddasa cututtuka, ciki har da sankarar mama.
Karin bayani:Nijar ta kori kamfanin Orano na Faransa
Tun a cikin shekarar 2015 Faransa ta haramta amfani da wannan sinadari, da ake amfani da shi wajen sarrafa robobin ruwan sha da sauran kayan zuwa abinci.