SiyasaFaransa
Sarkozy zai gurfana gaban kuliya a 2025
August 25, 2023Talla
A shekara ta 2025 ne dai ake sa ran za a fara sauraron shari'ar da kuma shaidu, inda ake zargin Nicolas Sarkozy da ke zaman dan jam'iyyar masu tsan-tsan ra'ayin kishin kasa da wasu mutane 12 da hada kai suka karbar makudan kudi a hannun tsohon shugaban kasar Libiyan marigayi Muammar Gaddafi ba bisa ka'ida ba, domin daukar nauyin takararsa ta shugaban kasa a zaben shekara ta 2007.