Faransa ta nisanta kanta da zama kanwa uwar gami
August 28, 2023Shugaba Macron ya furta kalamun ne a yayin da yake ganawa da jakadun kasashen Afirka a birnin Paris, inda ya kara da cewa da akwai kasawar Faransa da ba ta kasance a ko ina ba, kana a cikin jawabinsa Macron ya ce ya kwan da sanin jami'an diflomasiyar Fransa a ko ina cikin duniya sun fuskanci tarnaki.
Karin Bayani: Sabuwar baraka tsakanin Nijar da Faransa
Shugaba Emmanuel Macron ya ce "Faransa da jami'an diflomaisyyarta sun kasance a cikin mawuyacin hali a wasu kasashen nahiyar Afirka a 'yan watannin nan, misali a Sudan da Faransa ta zama misali, bayan kwashe 'yan kasarta da wasu 'yan kasashen ketare, ko a Nijar inda yanzu hakan jakadanmu ke ci gaba da aiki da kuma ke saurarenmu a yanzu."
Karin Bayani: Kadawar guguwar sauyi a yammacin Afirka
Kalamun shugaban na zuwa daidai lokacin da guguwar juye-juyen mulki ke daukar dumi a yankin Sahel ciki har da Nijar, kasar da sojojin da suka kifar da gwamnati suka umarci jakadan Faransa da ya fice daga kasar a cikin tsukin sa'o'i 48, matakin da fadar gwamnatin Elysee ta yi fatali da shi.