Faransa ta kama mutuman da ya kai hari Lyon
May 27, 2019Talla
Hukumomin shari'a a kasar Faransa sun sanar da kame wani matashi dan asali kasar Aljeriya mai shekaru 24 wanda ake zargi da kasancewa mutuman da ya dana bam kirar gargajiya da ya jikkata mutane 13 a birnin Lyon a ranar Juma'ar da ta gabata.
Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito magajin garin birnin na Lyon Gerard Collomb na cewa maharin dalibi ne da ke karatun a makarantar koyar da ilimin konfuta da amma ba ya a cikin rijistan masu aikata laifuka na 'yan sanda.
Hukumomin shari'a sun kuma sanar da kama mahaifiyar maharin da wani dalibi dan makarantar sakandare dan asalin kasar Aljeriya da ke da kusanci da maharin.