Fara kada kuri'a a zaben kasar Indiya
April 7, 2014Talla
'Yan adawar kasar Indiyan dai na fatan lashe zaben da zai basu damar yin gagarumin sauyi a bangaren tattalin arzikin kasar. Gyare-gyare dai musamman a fannin tattalin arziki da samar da ayyukan yi da ababen more rayuwa na daga cikin burin jam'iyyar adawa ta Bharatiya Janata Party BJP ta sanya a gaba yayin yakin neman zabe. Hasashe dai na nuni da cewa kawancen jam'iyyar ta BJP zai iya lashe kuri'u masu yawa a zaben. Kimanin al'ummar kasar miliyan 814 da suka cancanci kada kuri'a ne ake saran zasu kada kuri'unsu a zabukan da za a kwashe tsahon makwanni biyar ana gudanarwa a fadin kasar ta Indiya da kuma ake saran bayyana sakamakonsa a ranar 16 ga watan Mayu mai zuwa.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Usman Shehu Usman