ICC za ta binciki zargin laifukan yaki a Falasdinu
June 26, 2015Talla
Kundin dai na kunshe ne da shaidun da zasu tabbatar da zargin kisan kiyashi da suke yiwa Isra'ila a farmakin da ta ke kaiwa a yankin Zirin Gaza da kuma Gabar Yamma da Kogin Jodan. A yanzu haka dai mai gabatar da kara ta kotun Fatou Bensouda za ta fara gudanar da binciken sharar fage domin tabbatar da zargin Isra'ila da aikata laifukan yaki a Falasdinun. Matakin na zuwa ne kwana guda bayan da wani bincike da Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar ya zargi Isra'ila da Falasdinu da yiwuwar aikata laifukan yaki a yayin yakin da suka gwabza da juna a yankin Zirin Gaza a shekarar da ta gabata ta 2014. Tuni dai Isra'ilan ta yi watsi da wannan batu tana mai cewa ita ba mamba ba ce a kotun ta ICC.