Falasdinu na son zama mamba a kotun ICC
January 2, 2015Talla
Jakadan Faladinu a zauren Majalisar Dinkin Duniya Riyad Mansour ne ya mika wadannan takardu a Juma'ar nan a mastayin matakin samun rijista na shiga kotun wanda zai bata damar neman a gurfanar da kowacce kasa da ta ke zargi da aikata mata laifukan yaki.
Wannan matakin na Falasdinu dai na zuwa ne bayan da ta gaza samun goyon baya na kasancewa kasa mai cikakken iko a wata kuri'a da aka kada a Majalisar Dinkin Duniya.
Tuni dai Izra'ila da ke zaman doya da manja da Falasdinu ta nuna rashin amincewarta da matakin Faladinun na shiga kotun, inda ta ke cewar za ta maida martani kakkausa muddin Falasdinu ta shiga kotun.