1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Falasdinawa na tserewa harin Isra'ila a Khan Younis

Zainab Mohammed Abubakar
August 9, 2024

Dakarun Isra'ila sun kaddamar da sabbin hare-hare a manyan yankuna da ke kusa da Khan Younis a kudancin Zirin Gaza, bayan sun ba da umarnin kwashe jama'a daga yankin.

https://p.dw.com/p/4jJA4
Hoto: Hatem Khaled/REUTERS

Khan Younis da ke zama gari na biyu mafi girma a Gaza, ya yi asara mai dumbin yawa sakamakon hare-haren jiragen yaki da kuma kutsen dakarun Isra'ila ta kasa tun a farkon shekarar da muke ciki. Yankin da kaza lika ke fuskantar karancin abinci da magunguna da ruwa mai tsafta, da sauran kayan jin kai saboda rikicin da kuma takunkumin Isra'ila.

Ma'aikatar lafiya a Gaza ta ce adadin wadanda suka mutu a cikin yankin kadai ya kusan kai 40,000 tsawon yakin watanni 10 tsakanin Isra'ila da Hamas. Rikicin yankin ya yi kamari tun bayan da aka kashe shugaban siyasar Hamas Ismail Haniyeh a ranar 31 ga watan Yuli a Iran, sakamakon wani harin da ake kyautata zaton Isra'ila ce ta kai, inda yanzu ake zaman dar dar na yiwuwar kai harin daukar fansa.

Shugabannin kasashen duniya na kokarin ganin an tsagaita wuta a Gaza. Da maraicen wannan Alhamis Isra'ila ta tabbatar da cewa za ta aika da masu shiga tsakani don tattaunawa ta kai tsaye tare da Hamas a matsayin martani ga shawarar Amurka da Masar da Qatar.