Fafutikar kare dabbobi a Katsina
December 14, 2016Wani mai fafutukar kare hakkin dabbobi a jihar Katsina ya kafa wata kunguya da ke yaki da cuta wa dabbobi inda ya ke fadakar da al'umma yadda ya kamata su ruka kulawa da dabbobinsu a matsayin dukiyar da Allah ya ba su walau 'yan kasuwa ko kuma masu kiwo.
Shidai wannan mai kare hakkin dabbobi Abu Dan Malan Karofi ya kan shiga kasuwannin siyar da dabbobi da yin taruka da makiyaya gami da shiga kafafen yada labaru ya na fadakar da jama'a kan illar cutar da dabbobi dan haka ya kafa kungiyar kare dabbobin.
"Na kafane saboda ina da sha'awar na ga dabbobi da tsintsaye duk an ba su hakkinsu ina kokarin na ga cewa na kyautata masu rayuwarsu yadda kowa ke jin dadi a duniya, da kuma makomata a lahira saboda so nake ko na mutu 'ya'yana su cigaba saboda sadakatur jariya".
A cewar Abu Dan Malam akwai doka da aka tanada dan kare dabbobi a Najeriya sai dai ba ta da karfi dan haka ya ke fata a tsananta dokar. Dabbobi dai halitune da ke jure dukkanin abun da me kula da su ke masu saboda ba su da bakin da zasu iya kai kara gaban mahukunta.